2023: Mata sun roki APC da Buhari a kan su tsayar da Osinbajo takarar Shugabanci kasa


Gamaiyar Ƙungiyar Mata masu Goyon Bayan Osinbajo, NCWO, sun yi kira ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da jagororin jam'iyar APC da su tsayar da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na yarjejeniya a jam'iyar.

Kamar yadda Jaridar Daily Nigerian ta rawaito:ta ke taron manema labarai a Abuja, Rabi Dauda, shugabar NCWO, ta ce Osinbajo na da basirar dai zai ciyar da ƙasar nan gaba.

Dauda ta yi kira ga jagorancin APC da ya tabbatar da cewa an yi adalci a zaben shugabannin jam'iya mai zuwa.

A cewar ta, Osinbajo shugaba ne da ya ke da tausayin talakawa da al'umma baki ɗaya, in da ta yi kira ga Buhari da APC da su tabbatar sun samar da yarjejeniya domin a tsayar da Osibanjo takara domin ci gaban ƙasar nan.

Post a Comment

Previous Post Next Post