Kundin tarihi: Tarihi Da Asalin Yadda Kano Ta Samo Sunanta


 Asalin sunan jihar Kano ya samo asali ne daga wani fitaccen jarumi mai suna Kano da suka zauna yankin na Kano.

Jarumin na daga cikin mutanen da suka taso daga garin Gaya suka tare a wannan waje domin albarkar da wannan waje ke da shi.

An bayyana cewa garin na Kano ya kafu kimanin shekaru 2000 da suka wuce, inda aka ce ya samo asali shekaru 400 kafin zuwan addinin Musulunci.

Tarihi ya nuna cewa asalin mutanen da suka fara zama a Kano makera ne da suka taso daga garin Gaya a kokarinsu na neman kasa mai arzikin tama, wacce za su dinga sarrafata su dinga yin karfe da ita.

Wadannan makera sunyi dace da samun kasa mai wannan arziki, bayan arzikin tama da suka samu, sun kuma samu kasar mai ciki da albarkar noma da ruwa mai yawa ga dazuka masu yawa da za su iya fita farauta.

Zamanin da Kano cike take da tsaunika

A wancan lokacin wajen ya kasance mai matukar tsaro, domin kuwa akwai manyan tsaunika da duwatsu wadanda mutane za su iya hawa su buya idan abokanan gaba sun kawo musu hari.

Wadannan duwatsu sune irinsu Dutsen Dala, Goron Dutse, Dutsen Fanisau, Jirgirya da kuma Magwan.

Akwai kuma kogi da ruwa ke wucewa daban-daban da suka zagaye yankin, da suka hada da kogin Jakara da kuma kogin Kano.

Dalilin wannan arziki da albarka da wannan yanki yake da shi ya sanya mutane suka dinga yin kaura daga garuruwansu suna zuwa wajen domin cigaba da rayuwa.

Shin kun san cewa sunan wani barde ne Kano?

Daga cikin mutanen da suka fi shahara a wannan waje akwai wani fitaccen jarumin mafarauci mai suna Kano, wannan suna na jarumin shine asalin sunan da aka sanyawa garin na Kano, tun daga wanan lokacin aka fara kiran wannan gari da Kano.

Har yau ba a san lokacin da mutane suka fara zama a Kano ba

Wani masanin tarihin masarauta dake jami’ar Bayero ta Kano, Dr. Tijjani Muhammad Naniya, ya bayyanawa BBC Hausa cewa har ya zuwa yanzu masana ba su kai ga gano lokacin da mutane suka fara zama a yankin na Kano ba.

Haka kuma ya ce, masanan basu tantance mutanen wace Gaya ce suka fara zama a wannan waje ba. Ya ce akwai Gaya ta jihar Kano, akwai ta jamhuriyar Nijar da kuma ta yankin jihar Sokoto.

Babu wani cikakken bayani game da lokacin da mutane suka fara zama a yankin Kano, amma dai Dr. Naniya ya ce an taba gano wata makera a kusa da Dutsen Dala da masana suka bayyana cewa ta kai shekara 200 bayan zuwan Annabi Isa.

Wannan daliline yasa wasu masana ke cewa garin na Kano ya samo asali kimanin shekaru 400 kafin zuwan addinin Musulunci. Ma’ana yanzu birnin na Kano ya kai kimanin shekaru kusan 2000 da kafuwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post