SANSANIN MABARNATA A JIHAR KANO daga Maje Alhajij Hotoro


An samu wasu gungun mutane suna ta jidar 'ya'yan jihar Kano suna kaiwa Kudu ana cinikin su kamar awakai. An sauya musu suna da addini an ketawa wasu daga ciki rigar mutunci, an yi garkuwa da su an kuntata wa rayuwarsu.

Zuwa yanzu ba wanda zai ce ga takamaiman hukunci ga wadannan azzalumai, face iyayen yaran sun kafa kungiya suna ta taruka, ba wata kwakkwarar diyya sai jan kunnen kada su sake yaran su yi magana da 'yan jaridu.

Rundunar 'yansandan jihar Kano sun yi holen wani babban tantiri da ya mallaki asibitin kyankyasar jarirai wanda ake daukar nauyin mata a yi musu ciki su haihu a karbi 'ya'yan. Ko ina batunsa ya kwana?

Masu unguwanni da dagatai zuwa hakimai an jingine su a gefe, dillalai ne ke cin karensu ba babbaka. Da ka shigo Kano ka same su zasu ba ka gida ka biya hade da kudin takalmi ba ruwansu da me ka zo wanene kai?

Kowa ya zo burinsa a kai shi unguwar da ba ruwan kowa da kowa ba sa ido, don ya samu ya sake ya mike kafa ya shuka tsiyarsa. Wannan ya sa irin wannan unguwanni sun fi darajar kudin haya a Kano.

Unguwanni da dama na nan sun samu 'yancin cin karnuka babu babbaka, sakamakon dandazon mata da maza da suka fake da sunan 'yan Kannywood ne, ana tata tsiya da tsiyaya da sunan su 'yan fim ne don haka kowa da kowa ya samu mafaka tunda su masu masoya ne. 

Akwai unguwar da ta samu lasisin sheke aya tare da cin duniya da tsinke saboda an fake da sunan dalibai ne da suke zuwa karatu daga jihohin dake makotaka da jihar. Haya na matukar tsada a wajen yayin da madarar iskanci da sharholiya yake da matukar araha.

Masu unguwanni basu san su waye a unguwar su ba, kowa zai iya zuwa ya zuba uwar kuÉ—i ya sayi gona ya yanka ya fitar da filaye ya sayar wa kowa. Kowa zai iya gina gida ya bayar haya ga kowa. Makarantun kuÉ—i suna nan rututu ba wanda ya san hakikanin abubuwan da ke gudana sai Allah.

Post a Comment

Previous Post Next Post