Ba A Taba Yin Gwamnati Me Kyau Kamar Ta Buhari Ba, Ministoci


Yayin da Ministoci ke ajiye aikin su, biyo bayan umurni a gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari don sake shiga kakar zabe, sun bayyana cewa, ba a taba yin gwamnati kamar irin ta wannan shugaban kasa ba.

Har wa yau, ministocin sun yi godiya ga shugaban bisa basu damar kawa ci gaba da kima yin gagarumar gudummawarsu wajan yiwa kasa aiki.

Ministoci kimanin mutum 10 ne suka ajiye mukamansu, sun kuma bayyana hakane ta hannun minista a yankin Naija Delta, Godswill Akpabio.

Inda a karshe, Abubakar Malami nan take ya tabbatar da janyewa daga takarar gwamnan jihar Kebbi don ci gaba da rike mukaminsa na Minista.
 

Post a Comment

Previous Post Next Post