Shugaba Buhari Ya Cire DG NYSC Daga Mukaminsa.


Daga Abdulnasir Yusuf Ladan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kori babban darakta janar na hukumar yi wa kasa hidima NYSC, Birgediya Janar Mohammed Fadah.

Korar Mohammed Fadah din na zuwa ne watanni shida kacal da nada shi a matsayin shugaban na hukumar ta NYSC da aka yi a watan Mayu, 2022.

Sai dai da wakilin majiyar DCLHausa ta jaridar Punch ya tuntubi mai magana da yawun hukumar ta NYSC, Eddy Megwa, sai ya bukaci da ya jira za a fitat da sanarwa a hukumance da za ta fito a ranar Juma’a.


Inuwar Labarai RPT 001

Post a Comment

Previous Post Next Post