CIN ZARAFI: Wata Yarinya Yar Shekara 11 Ta Rasu A Garin Jos.

Daga Comrd Yusha'u Garba Shanga

Wata yarinya ‘yar shekara 11, mai suna Margaret Joshua ta rasu a garin Jos sakamakon cin zarafi da daga mairiÆ™onta. Misis Nneamaka Nwachuku, Æ™aramar hukumar Jos ta Kudu a Filato. 

Vanguard ta rahoto cewa wacce aka kashen ‘yar jihar Kebbi ce. Wace ake zargi da cin zarafin yarinyar tayi mata wani mummunar dukan tsiya ne inda a kullum take azabtar da ita har sai da ta mutu.
An yi zargin cewa bayan da aka yi wa yarinyar duka a baya-bayan nan, an tilasta wa yarinyar ta zauna a cikin kwantena da ruwan zafi wanda ya kona mata gaba, kuma ta rasu a asibiti a ranar Litinin, 14 ga watan Nuwamba.

Ko’odinetan hukumar kare haƙƙin bil’adama ta Æ™asa reshen jihar Filato, Grace Pam, wacce ofishinta ke bin diddigin lamarin ta shaida wa Vanguard cewa, bisa la’akari da yawan tambo da raunuka a jikinta, ya nuna cewa dole ne masu kula da ita sun yi mata wani mummunar gallazawa ne wanda bayada kima.
“Yayinda aka garzaya da kai ta asibitin Mandela da ke Kaduna kafin a tura ta zuwa Jos. Malaman asibitin sunyiwa Æ´an jarida bayanin kan lamarin a ranar Litinin da ta gabata, inda suka ce yarinyar ‘yar shekara 11 mai kula da ita, Misis Nneamaka Nwachukwu ta yi wa yarinya ‘yar shekara 11 mummunan duka ne tare da raunata ta a Vom shiyasa akai gamo da ajali har ta mutu. 

A lokacin da wasu ma’aikatan mu suka gana da wacce ake zargin Misis Nwachukwu a ofishin ‘yan sanda da ke Vom inda aka tsare ta, ta amsa cewa tana yi mata dukan tsiya gaskiya, kuma ta yi ikirarin cewa yarinyar batajin Magana don haka yasa ta hukunta domin ta daina.

Inuwar Labarai 

Post a Comment

Previous Post Next Post