JOS: Rikicin Kabilanci Ya Kaure A Shandam, an farfasa Masallacin Juma'a (Hotuna)

Kabilanci - Jos

 Rahotannin da muke samu sun nuna an fara nuna yatsa wa juna garin a Shandam dake jihar Filato, hakan ya samo asali ne kan rigimar neman mulki tsakanin kabilu biyu.


Yayin da ake ya gobe washe garin bada nadin sarauta a yankin ne rikici ya fara kaurewa, yayin da 'yan kabilar Ankwayawa dake da adadi mai yawa a yankin suka daki taburi da nuna rashin amincewarsu kan kara dora musu musulmi a Matsayin shugaba.


Wani rahoto da Jos Media News ta rawaito a ranar Asabar ya bayyana cewa, rigimar kuma ta fado garin Shandam ne, inda anan ne za a bada Sarautar kamar yadda aka saba. An shigo Shandam da zuga ta zanga-zangar kin amincewa da nada sarki musulmi.


Lamarin bai tsaya nan ba, ta kai ga an fara farfarsa wurare ciki har da babban masallacin Juma'a na garin Shandam dake jihar Filato.






Jihar Filato ta yi kaurin suna wajen yawan rikice-rikicen kabilanci, wanda a shekarar 2010 aka yi ta gwabza rikici tsakanin kabilu da hausawa lamarin da ya saka jihar shiga jerin wanda suka sami koma bayan tattalin arziki bayan kashe adadin mutane da dama sanadiyyar rikicin.


A baba-bayan nan, an kara samun wani mummunan lamari da ya faru a ranar Asabar, 14 ga watan Agusta, 2021, inda aka yi wa matafiya da ba su ji, ba su gani ba kisan gilla a hanyar Rukuba, kusa da Gada-biyu a Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato.


Lamarin ya harzuka dukkan musulman Nijeriya, duba da cewa matafiyar duk cikarsu Musulmai ne da suka fito tafiya.

Post a Comment

Previous Post Next Post