MATSALARKU TA ZO KARSHE: Maganin ciwon hakori mai karfin gaske

Ciwo-Hakori
Yadda Hakori ke yiwa marasa lafiya kogo

MAGANIN CIWON HAKORI

Assalamu alaikum masu bibiyar wannan shafi mai albarka, da fatan kuna cikin koshin lafiya. Yau muna tafe muku da maganin ciwon hakori ne kasidin, maganin gagajiya da zai tamaka muku wajen samun waraka kan ciwon hakori dake damunku.


CIWON HAKORI


Ciwon hakori wani bala'eh'en ciwo ne dake hana mutane sakat, da rawar gaban hantsi domin kuwa tafiyar su daya da 'yar karkare, innsuka kama mutum basu barinsa ta sauki.


Wanann yasa muka binciko tare da taco muku bayanin yadda zaku bi da amfani da maganin munna gargajiya don samun waraka da yardar Allah.


DA FARKO GA MAI CIWON HAKORI


A Sami Itacen Tumfafiya A Dafa Da Jar Kanwa a Kuskura da Dimin Shi Safe da Yamma Har Kwana 3, Haqora Zaa Warke.


KOGON HAKORI


A dibi Audugar Cikin Kwallon Tumfafiya a Dangwali Nonon ta Kadan a Sa Cikin Kogon, A Riqa Yin Haka Lokaci-Lokaci, Kogon Zai Cike, (Amma fa Akwai Zafi).


TSUTSAR HAKORI


A Tafasa Saiwar Tumfay a Kuskura da Dimin Shi, Sau 3 A Rana Kwana 2, za ka Rabu da Ita.


HAKORA MAI JINI


A Dafa Sassaqen Tumfafiya da Ganyen ta A Sa Gishiri Kadan, A Kuskura Baki da Dumi-Dumi Sau 3 A Rana Kwan 1 Zaayi, Haqora Za Su Daina Jini.


WARIN BAKI


A Dafa Furen Tumfafiya da Kwallon Ta Idan Ruwan Ya Huce A Sa A bin Wanke Baki (Brush) Ana Wanke Bakin Bayan an Dan Guntsi Ruwan, Kayi Ban Kwana da Doyin Baki.


HASKEN HAKORA


A Shanya Furen Tumfafiya Idan Ya Bushe A Maida Shi Gari A Hada Shi da Alif Kadan, A Dan Gwala da Buroshi ko Asuwaki A Wanke Baki,H akora Za suyi Fari Tas.


DATTIN GORO KO HAYAKIN TABA


A Dafa Furen Tumfafiya da Lemun Tsami (Lime) A Wanke Baki Dashi da a bin Wanke Baki (Brush), Dattin Zai Fita Daga Baki Gaba daya.


#RPT 002  

Post a Comment

Previous Post Next Post