SHARI'A DA LAUYOYI: Matar Da Ake Zargi Da Kashe Tsohon Mijinta A Jahar Kebbi Tana Cikin Tsaka Mai Wuya

Kisan-Kotu
Hauwa, Matar data kashe mijinta

Wata mata, Hauwa da ake zargi da kashe tsohon mijinta a garin Birnin kebbi ta kara shiga uku, inda kungiyar (NBA) Lauyoyin ta sha alwashi kanta da duk wanda ke da hannu a kisan Alkali Attahiru-Zagga.


Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) reshen jihar Kebbi, ta jajantawa iyalan marigayi Alkalin Alkalai Muhammad Attahiru-Zagga, wanda ake zargi da kashe shi a ranar Alhamis a Birnin Kebbi


Haka zalika kungiyar ta NBN tasha alwashin saita kwato ma iyalan wanda aka kashe hakken su na kashe mahaifin su, 


Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaranta, Mista Muhammad Usman, kuma aka rabawa manema labarai a Birnin Kebbi ranar Juma’a


Shi dai wanda aka kashe shine ya kasance Alkalin kotun Majistare ta 11 da ke Jega a jahar ta Kebbi, Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN ya bayar da rahoton cewa, har zuwa rasuwarsa, Attahiru-Zagga, wanda ya fito daga garin Zagga da ke karamar hukumar Bagudo a jihar, ya kasance Alkalin kotun Majistare ta II da ke Jega a karamar hukumar Jega a jihar Kebbi.


Kungiyar Lauyoyin ta sha alwashin zakulo masu hannu da wannan kisan da kuma ganin an hukunta su kamar yadda doka ta tanada.


#RPT 002
 

Post a Comment

Previous Post Next Post