AL'AJABI: Manomi dan shekara 67, ya auri mata 12, yana da ya'ya 102, jikoki 568

Musa Hasahya, Manomi mai mata 12, yara 102

 Wani Manomi dan kasar Uganda ya yi abin ban al'ajabi, ya auri mata 12 a rayuwarsa.

Magidancin mai suna, Musa Hasahya ya bayyana cewa; yanzu baya kalubalantar matansa kan amfani da magungunan hana haihuwa, a cewarsa gida ya yi masa yawa.

 Musa Hasahya ya fadi haka ne yayin da rayuwa ta fara yi masa tsada inda yake zaune da manyan ya'yansa a Bugisa, dake kasar ta Uganda.

Da ake zantawa da shi, magidanci mai ya'ya 102, Malam Musa ya bayyana cewa, yana fuskantar matsanancin tsadar rayuwa, duba da yadda hanyoyin samunsa suka yi kasa ga iyali sai kara girmama su ke yi.

Rahotanni daga Majiyar Inuwar Labarai sun jiyo cewa, Musa yana zaune ne a wani katafaren gida mai dakuna 12, inda aka tattara yana da tarin jikoki 568, kuma ya auri matarsa ​​ta farko, mai suna Hanifa ne a shakara ta 1971 lokacin yana da shekaru 16 a duniya.

Post a Comment

Previous Post Next Post