Yanzu-Yanzu: Gwamna Ganduje ya sanya Hannu akan kasafin Kudin shekarar 2023


Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya rattaba hannu a kan Kasafin kudin Shekarar baÉ—i, wanda Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ta Amince da shi a yau Alhamis,

Gwamnan ya Sanya hannun ne yayin taron Majalisar Zartarwar ta Jihar Kano Wanda ya gudana a dakin taron majalisar dake gidan gwamnatin jiha,

Jim kadan da Sanya hannu a kasafin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa yan majalisar bisa yadda sukai aikin kasafin kudin ba tare da bata lokaci ba, Wanda hakan zai baiwa Gwamnatin damar fara amfani da kasafin kudin a farkon sabuwar Shekara tun da ya Zama doka.

Gwamnan Ganduje yace bai yi mamakin yadda yan Majalisar suka kammala aikin na su da wuri ba, Inda yace zai tabbatar an yi aikin da kasafin kudin kamar yadda majalisar ta amince da shi.

Gwamnan ya yi alkawarin Ci gaba da baiwa Majalisar yancin cin gashin kanta, ba tare da tsoma baki a harkokin aikin Majalisar ba.

Ya kuma yaba da yadda Majalisar ta Gudanar da taron Jin ra’ayoyin al’umma akan kasafin, Inda ya bada tabbacin cewa Kasafin kudin zai fi mayar da hankali wajen kammala aiyukan da suka fara don gudun barin bashi mai yawa ga gwamnatin da za ta gaje shi, Inda yace kasafin kudin ya samu kari daga sama da Naira Biliyan 23.

Tun da farko a jawabinsaShugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Kano Hamisu Ibrahim Chidari yace sun Sami nasarar kammala aikin na su ne akan lokaci Saboda yadda Gwamnan ya gabatar musu da daftarin Kasafin akan Lokaci.

Post a Comment

Previous Post Next Post