DA ƊUMI-DUMI: Gwamna Ganduje ya Sallami kwamishinan Addinai Baba Impossible daga kan mukaminsa.

Gwamna Ganduje ya sallami Baba Impossible daga kan Kujerar Kwamishinan Addinai.

Cikin wata Sanarwa da Kwamishinan yada LABARAI na jahar Kano Kwamaret Muhammad Garba ya rabawa manema Labarai, yace Gwamnatin ta samu Baba Impossible wajen yin gaban Kasa na rage ranakun aiki ga Ma'aikan Ma'aikatarsa ba tare da tuntubar Gwamnatin ba wato ya rage musu ranakun Laraba da Jumu'a. 

Sannan Kuma baya biyayya ga Gwamnatin sau da Kafa.

Tuni dai Gwamnan ya aike da sunan Dr. Nazifi Ishaq Bichi na Jami'ar Bayero ga Majalisar Dokokin Jihar Kano Dan maye gurbin Baban.

1 Comments

  1. Allah ya sa wadda a ka daura ya zame mana mafi alkairi A Jahar mu baki daya

    ReplyDelete
Previous Post Next Post