DSS Sun Kama Editan Jaridar ALMIZAN, Ibrahim Musa


Jami’an tsaron farin kaya (DSS) sun kama babban editan fitacciyar jaridar Hausa, wato ‘ALMIZAN’ Malam Ibrahim a hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya domin yin Umrah.

Iyalan Musa, su ne suka sanar da kama shi ta cikin wata sanarwar da suka fitar a ranar Laraba, inda suka bukaci hukumar da ta gaggauta sake shi ba tare da wani sharadi ba.

Sanarwar wacce Abdullahi Usman ya fitar a madadin iyalan editan, sun ce, an kama Ibrahim Musa ne a filin sauka da tashin jiragen kasa da kasa ta Malam Aminu Kano da safiyar ranar Laraba a hanyarsa ta zuwa Saudiyya domin yin Umrah.

Sanarwar ta ce, Ibrahim yana tare da daya daga cikin ‘yan ahlinsa, Binta Sulaiman ne a lokacin da aka kama shi.

“Duk da har zuwa yanzu babu wasu dalilan da hukumomin suka bayar na yin awun gaba da shi. Don haka cikin gaggawa muna kira ga hukumomin nan da su gaggauta sakeshi ba tare da wani sharadi ba,” sanarwar ta shaida.

Sanarwar ta ce, Ibrahim Musa ya kasance dan gwagwarmayar nema wa raunana ‘yanci da kuma daga murya a duk lokacin da ya ga ana zalumtar wasu raunana.

Usman, ya kara da cewa editan ya kuma kasance mai nema wa daruruwan mutane da aka kama adalci a lokuta daban-daban, don haka ne ya nuna mamakinsu bisa kamun da aka yi wa dan jaridan.

Ita ma kungiyar kare hakkin bil-adama ta Amnesty Internatinal ta bukaci gwamnatin Nijeriya karkashin Bola Ahmed Tinubu da ta gaggauta sake Mallam Ibrahim Musa, wanda ya kasance shugaban kungiyar Media Forum na Harkar Musulumci a Nijeriya (IMN).

Amnesty ta wallafa a shafinta na X (da aka fi sani da Tiwuta) a ranar Labara, su ma masu kiran gwamnatin da ta sake editan jaridar na ALMIZAN cikin gaggawa ba kuma tare da wani sharadi ba.

©WikiTimes

Post a Comment

Previous Post Next Post