Editan Jaridar Almizan, Ibrahim Musa ya samu 'yancinsa daga hannun DSS


Daga Zailani Mustapha

Labarin dake shigo ma Jaridar MADOGARA a halin yanzu na nuni da cewa jami'an tsaron farin na kaya na Hukumar DSS sun saki Malam Ibrahim Musa, Babban Editan Jaridar ALMIZAN.

DSS sun kama Ibrahim Musa ne da safiyar jiya Laraba 27 ga watan Satumban 2023 a filin jirgin Malam Aminu Kano a yayin da yake shirin tafiya Umrah kasar Saudiyyah. 

A wata takardar manema labarai da iyalansa suka fitar dauke da sa hannun Abdullahi Usman, sun bayyana cewa: "muna sanar da cewa an saki Malam Ibrahim Musa, Babban Editan Jaridar Almizan, wanda hukumar tsaro ta DSS suka sace shi. 

Sanarwar ta kara da cewa; an sake shi ne a ranar Alhamis kuma tuni aka dawo masa da takardunsa na tafiya. 

"Yanzu haka yana tare da iyalansa da 'yan'uwa da abokan arziki cikin koshin lafiya. 

"Muna amfani da wannan dama wajen mika godiya ga kafatanin wadanda suka taya mu da addu'a da nuna damuwa bisa kamun da aka yi masa tare da tsare shi da DSS suka yi. Muna godiya gare ku baki daya, Allah ya saka muku da alherinsa", in ji sanarwar. 

©Jaridar Madogara 

Post a Comment

Previous Post Next Post