Hanyoyin Da Zaka Bi Ka Goge Account Ɗinka Na Facebook Bayan Mutuwarka.

Da yawan masu amfani da kafafen sadarwa na zamani za su so a ce suna barin duniyar nan, an goge shafukan su ba tare da la'akari da me su ka kasance suna yaɗawa a lokacin rayuwarsu ba. 

To ga yadda za ka yi tun yanzu da kake raye ka ɗora shafinka bisa wa'adin mutuwa lokaci guda tare da taka mutuwar 😭

Hanyoyin kuwa su ne:

1. Shiga "Settings and Privacy"
2. Sai ka shiga "Personal Settings"
3. Sai ka shiga "Account ownership and Control"
4. Sai ka shiga "memorialization" wato wajen da za ka zaɓi yadda kamfanin Meta za su yi da account ɗin ka bayan ka kwanta dama.
5. Sai ka zaɓi account ɗin da ke nuni da sunan ka a wajen da aka rubuta "Delete after death".

Shikenan! Da zarar ka saita account dinka a haka, Facebook algorithm zai gane ka mutu, sai ya goge account ɗin gaba ɗaya. 

Ta yaya zai gane?

Za su yi amfani da mashinshinin AI ne wajen gano saƙon ta'aziyya da kuma saƙonnin RIP da ake turawa mamaci.

Daga nan sai su goge komai naka.

Allah Ya sa mu cika da imani.

Ga misali;

©Yakubu Muhammad Rigasa


Post a Comment

Previous Post Next Post